Friday, April 3
Shadow

Tag: Adu’ar Neman Aure

Adu’ar Neman Aure: Hanyar Neman Miji ko Mata Nagari da Albarkar Allah (SWT)

Adu’ar Neman Aure: Hanyar Neman Miji ko Mata Nagari da Albarkar Allah (SWT)

Addu’o’in Al-Qur’ani
Aure na daga cikin manyan ni’imomin da Allah Madaukakin Sarki Ya tanadar wa bayinsa domin samun natsuwa, kwanciyar hankali, da cikar addini. Saboda haka, neman aure ba kawai al’amari ne na zuciya ko sha’awa ba, har ila yau ibada ce idan aka yi ta bisa tafarkin shari’a da kyakkyawar niyya. A yau, mun kawo muku Adu’ar Neman Aure, wacce take taimaka wa mace ko namiji wajen roƙon Allah Ya azurta shi da abokin rayuwa nagari, mai addini da tarbiyya. Wannan addu’a ta dace da namiji da ke neman mata, da kuma mace da ke neman miji, haka kuma ana iya yin ta domin nema wa ma’aurata samun haihuwa idan akwai jinkiri a wannan bangare. Duk wanda yake cikin wannan hali, zai iya dogara ga Allah Ya buɗe masa ƙofa ta alheri da sauƙi, domin Shi ne Mai amsa addu’a. Muhimmancin Yin Addu’a Wajen Neman Aure ...